Rundunar yansandan jihar Niger ta kama wata mata yar shekara 24 mai suna Amina Aliyu bisa zargin kashe Amarya da mijinta ya auro a jihar Niger.
"Ranar Talata wani mutum mai suna Bello Lawal da ke Gwari Motors Bosso road Minna, ya kawo Kara amadadin Alhaji Aliyu Abdullahi mai shekara 45 da ke zaune a Mandela road Sauka Kahuta, cewa an sami gawar matarsa kuma Amaryarsa mai suna Fati Aliyu jina jina, jikinta kuma a kone da wuta.
"Bayan samun wannan koke ne yansanda suka shiga aiki, kuma suka kama uwargidan mai suna Amina Aliyu yar shekara 24. Yansanda sun sami tabarya da ake zargin Amina ta yi amfani da shi ta kashe Fatima saboda yar uwar Amina ta shaida wa yansanda haka, kuma shaida ce domin a gaban jdonta lamarin ya faru.
Yansanda sun dauki tabarya da ake zargin Amina ta kashe Fatima da shi, kuma za mu gurfanar ta Ammina a gaban Kotu da zarar mun kammala bincike" Inji DSP Wasiu Abiodun.
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari