Gwamnatin Kano Tace ta ƙwace filaye kimanin 400 daga Hannun Mutane


Hukumar dake kula da ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci ta jahar Kano (PCACC) ta ƙwace filaye kimanin 400 daga hannun wasu mutane a faɗin jihar. Jaridar legit ta ruwaito.

Ta kuma bayyana cewa yawan filayen ta ƙwace su ne ta maidama asalin waɗanda suka mallaki filayen, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana haka a wani taron haɗin guiwa da ya gudana a hedkwatar hukumar ranar Laraba.

Shugaban ya ƙara da cewa hukumarsa ta ƙwato maƙudan kuɗaɗe da suka wuce N521,964,122.

Rimingado, ya bayyana cewar hukumar su ta samu korafe-korafe 2256 daga wajen jama'a cikin wannan shekarar da muke ciki.

Ya ce hukumar ta samu nasarar gano wuraren ajiya inda aka ajiye kayayyaki masu muhimmanci na biliyoyin nairori da aka kwace amma daga baya aka sake su bayan tattaunawa da yan kasuwar.

Rimingado yace:

"Mun kwato filaye 400 daga hannun wasu mutane kuma mun maida su ga asalin waɗanda suka mallaki filayen a sassa daban-daban na jihar nan."

"Mun kuma shiga tsakani, mun sulhunta matsalolin tsaro 60 tsakanin makiyaya da manoma, wanda mafi yawancin su a kan kiyo ne."

Rimingado yace dayawan mutane ana kaisu kotu kan rikicin da basu ji ba basu gani ba, musamman a ƙananan hukumomin Ɗanbatta, Ɓagwai da Kuma Tudun Wada.

Ya kuma ƙara jaddada cewa hukumar su zata cigaba da aiki yadda yakamata don ƙara tabbatar da Kano a cikin jihohin farko a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN