Type Here to Get Search Results !

Zancen Nayelwa da Gulumbe: Abin da ya kamata ku sani


Shafin ISYAKU.COM na sanar da masoyanmu cewa ranar 19 ga watan Maris, mun daga wasu labarai guda biyu daga wani shahararren gidan rediyon FM mai matukar tasiri da farin jini ga al'umma na labari dangane da zargin harin yan bindiga a garuruwan Nayelwa da Gulumbe a jihar Kebbi.

Muna sanar da masoyanmu masu wadataccen hankali da bayyanannen adalci cewa yau mako biyu kenan babu wanda ya rubuto mana koke, shawara ko akula dangane da cewa akwai kuskure a labari amma wanda ya yi nuni da shigan Yan bindiga a garin Gulumbe wanda muka gano cewa kuskure aka samu daga gidan rediyon FM da ta fara labarta lamarin tun farko.

Kasancewa babu wani koke da muka samu daga jama'an Gulumbe kan labarin bisa ka'idar tsarin shafinmu. Duk da yake mun samar da gurbi da ya kamata a sanar da mu ta hanuyar aika koke, abinda aka kula, shawara ko ra'ayi dangane da labaranmu amma ba a yi amfani da wannan damar ba.

Muna tunatar da jama'a cewa shafin labarai na ISYAKU.COM tare da wasu shafukan Turanci da Hausa na wallafa labarai tare da gudanar da ayyukan fasahar zamani na wayar salula da ingizon yanar gizo, masana aikatau da kera manhaja ne wadda ke da cikakken rijista da hukuma bisa lambar kampani RC 1470216.

Sai dai bayan mun wallafa labari tun karfe 10 na safe, mun sami kiran wani dan soshal midiya, shi kwaya daya tilau,  wanda ya dinga kalubalantar mu da karfe 10 na dare a wayar salula ba tare da bin ka'idar rubuta koke ta shafin labari da yake mag44ana a kai ba. Mun gano cewa manufar wasu mutane ba wai a yi gyara bane, illa dama ce da suka kirkiro domin su isar da wata manufa.

Kafar labarai da ta yi kuskure wajen wallafa labari, ita ke da hakkin gyara labarin matukar akwai kuskure a labarin. Domin ba mamaki ta wanan kafa jama'a suka samj labari saboda baka ya kamata su gan gyara ta wannan kafar.

Kowane kafar labarai kan yi kuskure daga lokaci zuwa lokaci, da jama'an Gulumbe ma'abuta wadataccen hankali da ingantaccen mutun sun rubuta koke cewa akwai kuskure a labarin, tabbas cikin minti 5 za a gyara har da ban hakuri.

Sai dai shafin labarai na ISYAKU.COM na sanar da jama'a cewa Babu ganganci ko wata manufa a labari da muka wallafa dangane da lamarin, sai dai tunda yan soshal midiya sun yi iya abin da suka iya na kalamai da suka wadatu da tunani da tsarinsu. Kenan sun saka wa kansu da wadanda suka sa su.

Muna matukar godiya ga ma'abuta kyawawan zukata ta suka iya banbancewa tsakanin KUSKURE da KARYA, tsakanin NEMAN GYARA da kuma NEMAN SUNA. Allah ya saka ma wadanda suka fahimce mu da alhairi.

Mun gode.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies