Mahaifi Ya Kashe Ɗansa Ta Hanyar Lakaɗa Masa Duka a Kano


Rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Jaridar legit ta ruwaito cewa mahaifin ya yi wa dansa duka ne kan zarginsa da sace masa kaya a shago

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

"Muna zaune a cikin shago a nan wurin sai muka ji yana dukan yaronsa a cikin shago, sunan shi Auwalu amma an fi saninsa da Abba, mun tsaya a waje a nan wurin yana ta dukan yaron badai wanda ya je wurin sai makwabcinsa mai wankin hula, ya zo ya same shi, ya ce mishi ... ya dai masa magana, ni banji abinda ya fada masa ba, amma na ji lokacin da shi mahaifin ya ke masa tsawa ya ke ce masa ya fita masa a shago, ganin haka yasa muma ba mu tafi wurin ba," a cewar Kabiru

Hajiya Goshi Muhammad, mahaifiyar yaron wadda ta dade da rabuwa da mahaifin tsawon lokaci ta ce yaron ya zo mata cikin mawuyacin hali ta tambaye shi abinda yafaru, sai ya fada cewa mahaifinsa ne ya doke shi saboda wai bai ga 'mansa ba guda biyu'.

Yaron ya shaidawa mahaifiyarsa cewa mahaifinsa ya yi ta dukansa a kai da ciki duk da cewa ya fada masa ba shine ya sace kaya a shagon ba.

Rundunar yan sandan Kano ta bakin kakakinta ya ce mahaifin yaron yana hannunsu,an mika shi sashin binciken manyan laifuka, bangaren kisar kai ana cigaba da bincike a kansa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN