Yan bindiga da ake zaton masu sace mutane ne, sun kashe yansanda guda hudu a wajen binciken ababen hawa na yansanda, a birnin Calabar a jihar Cross Rivers.
Mun samo cewa lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar Alhamis 25 ga watan Fabrairu.
Mun kuma samo cewa Yan bindigan sun yi wa yansandan kwanton bauna ne a Ayanmbat da ke kusa da Idundu a unguwar Aka Efaka a Birnin Calabar.
An ce yansandan sun gamu da ajalinsu ne, yayin da suka je domin su kubutar da wasu da ake zargin an sace su domin a karbi kudin fansa.
Bayanai sun ce yansanda sun dukufa domin gano wadanda suka aikata wannan ta'asa
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari