Bakwai daga cikin yara mata yan makaranta guda 317 da aka sace a makarantar mà ta da ke Jangebe a jihar Zamfara sun gudu daga hannun wadanda suka sace su, Channels TV ta là barta.
Ana zargin cewa yan bindiga ne suka sace su da sanyin safiyar ranar Juma'a 26 va watan Fabrairu.
Channels TV ta ce wani mazauni yankin da lamarin ya faru ya rada mata cewa hakika yaran guda 7 sun dawo gida da yammacin ranar Juma'a 26 ga watan Fabrairu.
Ya ce yaran sun sami sace jiki ne yayin da suke tafiya a cikin gandun daji kuma suka tsere..
Ya ce ana sa ran cewa akwai Karin wasu yaran da suka tsere kuma ana sa ran isowarsu gida.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari