Yan sanda sun fatattaki masu garkuwa da mutane a Zamfara, sun kwace babura da makamai


Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun samu nasara dakile wani mumunan harin da yan bindiga da fashi da makami suka kai jihar Zamfara.

Kwamishanan yan sandan jihar, Yaro Abutu, a ranar Talata ya bayyana irin makamai da kayyayakin Sojojin da aka kwato daga wajen yan bindiga.

A cewarsa, yan bindiga sun gudu sun bar baburansu akalla 14 yayinda yan sanda suka bude musu wuta.

Hakazalika an gano kayan Sojojin jamhuriyyar Nijar a wajen yan bindigan wanda suke amfani da shi wajen badda kama.

Yaro ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Gusau, babbar birnin jihar Zamfara, TVC News ta ruwaito.

"Mun kwato wadanda baburan ne daga wajen tsagerun yan bindiga, wanda suka gudu yayinda yan sanda suka kure musu gudu. Da yawa cikinsu sun jigawa," ya bayyana.

"Bayan haka, mun gano kayan Sojoji dauke da tambarin hukumar Sojin jamhuriyyar Nijar."

Shi kuwa kwamishanan tsaron jihar Zamfara, Abubakar Dauran, ya jaddada muhimmacin sulhu da yan bindigan domin tabbatar da zaman lafiya cikin al'umma.

Saboda haka, ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa maso yamma musamman Kastina, Kebbi, Sokoto, Neja da Kaduna su bi sahun jihar Zamfara don kawo karshen matsalar tsaro.

A wani labarin kuwa, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mataimaki na musamman ga Mataimakin Gwamnan Taraba, Alhaji Bala Baba.

Wata majiya daga danginsa ta shaida wa jaridar The Nation cewa an sace Bala ne a gidansa da ke yankin Sabongari na Jalingo da misalin karfe 1.30 na safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu.

A cewar majiyar, 'yan bindigar sun mamaye yankin, inda suka yi ta harbi ba kakkauta na sama da mintuna 30 kafin suka tafi da shi.

Source: Legit Nigeria


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN