Ayarin motocin Zulum sun yi hatsari, mutum 2 sun rasa rayukansu

Mutane biyu sun mutu sakamakon hatsarin da ya cika da ayarin motocin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum Jaridar legit hausa ta ruwaito.

Jaridar TheCable ta fahimci cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri.

Zulum na dawowa ne daga karamar hukumar Mafa (LGA) inda ya je sabonta rijistarsa na dann jam'iyyar All Progressives Congress (APC) lokacin da hatsarin ya faru

Wata majiyar ‘yan sanda da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce wani basarake na daga cikin wadanda suka mutu

A cewar 'yan sandan, motar da ke dauke da Mai-Kanuribe, wani hakimin Borno da ke Legas, ta kife bayan da tayar ta fashe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa da kuma wani fasinja guda daya.

An garzaya da mutane biyu da suka jikkata zuwa asibiti yayin da aka kai gawarwakin mutanen biyu da suka mutu zuwa Maiduguri.

Wannan lamarin ya zo ne watanni hudu bayan maharan Boko Haram sun kai wa ayarin motocin Zulum hari sau biyu a cikin mako guda.

A wani labari na daban, Fulani makiyayan dake kudu maso yamma, kudu maso gabas da wasu sassan Najeriya sun bayyana niyar komawa jihar Kano inda aka shirya musu shirin RUGA.

Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a jihar Kano, Zubairu Ibrahim, ya bayyana hakan.

A cewar Ibrahim, makiyayan sun hada wadanda ke zaune a jihar Nasarawa, Neja, Enugu, Oyo, da sauran su.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN