Yan bindiga sun kashe mutane 7 a garin Unashi Masarautar Zuru



Rahotannin daga garin Unashi da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi sun ce yan bindiga sun kashe mutane 7  a wani harin bazata ranar Juma'a 5 ga watan Fabrairu da karfe 12 na rana.


Majiyar mu ta ce jami'an soji tare da taimakon Yan sa Kai sun fuskanci yan bindigan suka kore su tare da yi masu mumunan barna.

Mun samo cewa yan bindigan sun kashe bayin Allah da suka hada da 


1 Bilyaminu Yahaya
2 Mukhtar Yahaya
3 Musa Moh Chinoko
4 Abubakar Kungiya
5 Barka Dan madami
6 Ahada Tanko
7 Gudaje Girmace


Rahotun ya nuna cewa ba a barnata dukiya ko gidaje ba a harin na yan bindiga a garin Unashi ranar Juma'a.


Idan baku manta ba, a watan Disamba 2020, yan bindiga sun kashe mutane 14 a garin Yarkuka da ke makwabta da garin Unashi kamar yadda majiyar mu ta shaida mana.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN