Wata Lauya wacce ke dauke da juna biyu mai suna Nkiru Agbasu ta mutu bayan wasu matasa da ake zargin yan fashi da makami ne sun bude wuta kan motar da Nkiru ke ciki a kan tagwayen hanyar Warri zuwa Sapele a jihar Delta.
Shafin ISYAKU COM ya samo cewa Nkiru ce kawai ta mutu a cikin motar ta fasinja, bayan yan fashi dauke da bindigogi sun buda wa motar haya wuta yayin da motar ke kan hanyarta ta komawa Warri daga garin Sapele.
Emmanuel O. Uti, shugaban kungiyar Lauyoyi reshen Warri, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace " Tabbas lamarin ya faru. Fashi da makami aka yi wanda ya rutsa da ita bayan yan fashin sun harbi motar haya da take ciki. Ita kadai ce harsashi ya sameta kuma ta mutu.
Mun Sami labarin faruwar lamarin ne da karfe 5 na yamma, wata kila abin ya faru ne tsakanin rana zuwa yamma".
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari