Wata Kotun Majistare a gundumar Bushenyi ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu, ta tasa keyar wata budurwa zuwa Kurkuku bayan ta kashe saurayinta.
Alkalin Kotun Majistare Paul Osauro, ya tasa keyar Loyce Tihainomwangire zuwa Kurkuku bayan yansanda sun gurfanar da ita a gaban Kotu bisa zargin kashe saurayinta Allan Mandela mai shekara 26 a Duniya bisa zargin cin amanarta.
Mai gabatar da kara Sylus Bwambale ya gaya wa Kotu cewa Tihainomwangire ranar 12 ga watan Fabrairu 2021, lokacin da take Kitwe, Rwentuha a garin Bushenyi, ta kashe Mandela, mai aikin gabatar da shirin wasanni a gidan rediyon Hunter FM.
Sai dai sabbin rahotanni sun ce Tihainomwangire ta gaya wa CID masu bincike cewa ta kashe Allan ne saboda ya sa mata cutar HIV da farko, amma bayan CID sun kaita Asibiti aka yi gwaji, sai sakamakon gwaji ya nuna cewa bata dauke da cutar HIV. Daga bisani sai ta canja bayani da ta rubuta wa CID, ta ce ta kashe Allan ne saboda yana shirin auren wata yarinya, kuma har shirin ya yi nisa.
Alkalin Kotun, Osauro, bai bari wacce ake zargin ta ce komi ba a cikin Kotu bayan mai gabatar da kara ya karanta laifin da ake tuhumarta da aikatawa, daga bisani ya bayar da umarnin tasa keyarta zuwa Kurkukun Gwamnati a garin Nyamushegyera har zuwa ranar 29 ga watan Maris 2021, ranar da Kotu za ta ci gaba da shari'ar.
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari