Uwargida ta make maigida da katako a kai ya mutu, karanta dalili


Rundunar yansandan jihar Ondo ta kama wata matar aure mai suna Queen Beatrice bisa zargin kashe mijinta mai suna Emmanuel Ekujuni a garin Omotosho da ke karamar hukumar Okitipupa.

Shafin ISYAKU COM ya samo cewa rikici ya tashi ne bayan Emmanuel ya kira wata mata a wayar salularsa kuma a gaban matarsa Beatrice, sakamakon haka rikici ya kaure har Beatrice ta dauki Planki ta kawada wa mijinta Emmanuel a kansa, lamari da ya yi sanadin mutuwarsa.

Kakakin yansandan jihar Ondo ASP Lee Teo Ikere ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yansanda na gudanar da bincike.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN