Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya yi zargin cewa mata masu tallar Fura da Nono na yi wa ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda a Jihar Sakkwato safarar miyagun kwayoyi Jaridar Aminiya ta wallafa.
Gwamnan ya yi furucin haka ne ranar Asabar yayin da fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmed Gumi ya jagoranci shirin karbar tuban ’yan bindiga da aka yi wa lakabi GULBAR a birnin Shehu.
“Wani takawarana, wani gwamna mai ci ya taba bani labarin wani abun da ya faru. Ya gaya mani cewa ta taba ziyartar wani kauye yana son sayen nono a wurin matan kauyen da suke fita cin kasuwar sayar da fura da nono.”“
Lokacin da ya kira su, sai daya daga cikinsu ta tsere. Ya tambayi mene ne yake faruwa sai aka fada masa cewa ai ba tallar nono ta dauko ba face miyagun kwayoyi ne a cikin kwaryarta.”
“Ya gaya mani cewa yawanci ’yan bindiga da masu satar mutane da sauran ’yan ta’adda suna samun miyagun kwayoyi ne ta wannan hanya.”
“A saboda wannan dalili, dole ne mu tashi tsaye domin shawo kan wannan matsalar ta sha da fataucin miyagun kwayoyi, don idan ba haka ba za mu karasa kashe macijin ne ba tare da sare kansa ba,” in ji Gwamnan.
A cewarsa, “ya kamata mu lura da irin rawar da miyagun kwayoyi ke takawa wajen rura wutar ta’addanci da sauran munanan halaye.”
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari