Miyar Kuka na kara wa mata ni’ima da kara karfi ga maza - Nazari


Wani rahoto da muka samo daga BBC Hausa ya nuna cewa, kuka bishiya ce mai asali da ake samu a nahiyar Afirka da kuma wani yanki na kasashen Larabawa. A al’adance bishiyar kuka tana da matsayi da muhimmanci ga abinci da magungunan mutanen Afirka. Kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya, kamar yadda mujallar lafiya ta Healthline ta bayyana a wani bincikenta game da amfanin kuka ga lafiyar dan’Adam. Tun daga ganyen kuka da bawon da yayan kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum.

Mujallar ta ce, kuka tana kunshe da kusan dukkanin sinadaran da jikin mutum yake bukata. Kuka na da sinadarin Calcium da ke taimakawa wajen kwarin kashi da hakori da sinadarin magnesium wanda yake daidaita jini. Kuka tana kuma da sinadarin iron wanda yake kare jiki daga kamuwa da cutar rashin jini, haka kuma kuka tana da sinadarin potasium da ke sasaita jini. Sannan uwa-uba sinadarin bitamin C ya fi yawa a kuka wanda ke yaki da cututtuka. Sauran sinadaran da ke cikin kuka sun hada da sinadarin cabonhydate da protien da bitamin D da kuma sinadarin fibre da ke sa abinci saurin narke wa a jiki.
Babban Sinadarin Da Ke Cikin Kuka
Bincike ya nuna kuka tana samar da kusan rabin sinadarin bitamin C da jikin mutum da ya haura shekara 18 ke bukata.
Maijidda Badamasi Shu’aibu Birci malama kuma kwararriya kan abinci mai gina jiki ta ce, wani binciken masana ya gano cewa kuka ta fi lemun zaki sinadarin bitamin C da linki 10, haka ma lemun tsami.
Mujallar lafiya ta Healthline ta ce, kuka tana dauke da kashi 58 na bitamin C da mutum yake bukata a rana.
Malama Maijidda ta ce, zaren kuka ya fi yawan sinadarin bitamin C, inda ta ce ana amfani da shi ga masu kansa.
“Mun taba amfani da zaren kuka ga mai cutar kansa,” in ji ta.
Amfanin bitamin C Ga Jikin dan’Adam Ya Hada Da
bitamin C sindari ne da ke kare kwayoyin halitta da kiyaye su cikin koshin lafiya.
Yana kara lafiyar fata da hanyoyin jini da lafiyar kashi da kuma bargo
bitamin C na taimakawa wajen saurin warkewar ciwo.
Masana sun ce ga ka’ida ‘yan shekara tsakanin 19 zuwa 64 suna bukatar 40mg na bitamin C a rana. Kuma an fi samun sinadarin bitamin C a abincin da mutane suke ci wanda ana bukatar sinadarin a kullum.
Tun daga daga ganyen kuka da bawon da ‘ya’yan kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum. Miyar Kuka ta fi dukkanin sauran gayyakin da Hausawa ke miya da su amfani ga jiki saboda yawan sinataran da take dauke da su, a cewar masana.
Malama Maijidda kwararriya kan abinci mai gina jiki ta ce kuka ta fi alayyahu da kubewa cikin ire-iren gayayyaki da ‘ya’yan ita ce da Hausawa ke yin miya da su a abinci. Malamar ta ce, yadda mutanen kauye ke yawan shan kuka yana kara masu lafiya, “shi ya sa yawancin cutukan da ake yi a gari da wuya a same su kauye.” Ta ce, kuka tana warkar da cututtuka da dama kuma mutane ba su san amfanin kuka ba ne ya sa suke gujewa amfani da garinta ko ganyenta musamman a abinci.
Maganin Da Kuka Take Yi
Kuka tana maganin zazzabin maleriya
Kuka tana maganin tarin fuka TB
Tana kara ingana garkuwar jiki
Kuka tana kara jini a jiki
Kuka tana maganin gudawa
Kuka tana maganin hakori
Kuka tana maganin ulsa
Kuka tana rage kiba
Baya ga wadannan, malama Maijidda ta ce idan ana shan kuka ba zai sa mutum ya samu kumburin ciki ba saboda rashin narkewar abinci sakamakon sinadarin fibre da ke cikinta. Haka kuma ga wadanda ke son rage tumbi ana iya shan ganyen kuka domin yana narkar da kitse.
Masaniyar ta ce kuka tana maganin ciwon ulsa – “ga mai ulsa zai kada ganyen kuka a ruwa a sha, cikin lokaci kadan zai samu saukiin ulsa.”
Kuka Tana kara Ni’ima Ga Mata Da Mazakuta Ga Maza
Masana sun ce, saboda tasirin kuka wajen inganta ruwan jikin mutum, tana kuma tasiri wajen kara ni’ima ga mata.
Yadda ya kamata mata su yi amfani da kuma a cewar malama Maijidda, za a samu sassakin kuka a wanke sosai sai dinga sha kofi daya da safe da yamma. Sannan ta ce, kuka tana kara wa maza karfin jiki da mazakuta. Haka kuma mazan da ke son jikinsu ya bude kuka tana taimakawa saboda sinadaran da ke cikinta.
Yadda Ya Kamata A Yi Amfani Da Kuka
Ana busar da ganyen kuka a nike a tankade a yi miya domin cin tuwon dawa ko masara ko shinkafa ko alkama. Kamar yadda aka yi bayani tun a farko cewa kuka tana da matsayi musamman a abincin Hausawa.
Hausawa suna yin miya da ganyen kuka. Ana busar da ganyen kuka a nike a tankade a yi miya domin cin tuwon dawa ko masara ko shinkafa ko alkama. Haka kuma Hausawa sukan yi amfani da kuka wajen yin danwake. Amma masana sun ce danyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka da ake miya da shi.
Malama Maijidda ta ce, yadda ake busar da kuka yana kashe wasu sinadaran da ke kunshe a cikinta, saboda rana da aka shanya kukar tana kone sinadarai da dama.Ta ce danyen ganyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka karin lafiya da sinadarai a cikin miya. Sannan ba a son idan za a yi miyan kuka a bari ta sha wuta sosai domin yawan dafuwa zai rage yawan sinadaran da ke cikin kuka, a cewar malama Maijidda.
Shin Ko Kuka Na Da Wata Illa?
Masana na ganin duk da ba a zurfafa bincike ba kan kuka, kamar yadda ake bukatar binciken sosai game da bishiyar mai matukar muhimmanci ga lafiya, amma zuwa yanzu babu wata babbar illa a kuka. Sai dai duk lokacin da mutum ya fahimci wata matsala bayan amfani da ganye ko garin kuka an fi son a ziyarci likita musamman mata masu juna biyu da shayarwa. Haka kuma kamar yadda aka yi bayani cewa kuka tana da sinadarin bitamin C sosai, amfani da ita da yawa yana iya haifar da ciwon ciki ko gudawa idan har mutum ya yi amfani da adadin kuka da ya wuce kima.
Masana sun yi gargadi cewa kada mutane don sun ji an ce kuka tana da sinadarai sosai ga lafiyar jiki su dinga sha da yawa. Domin sha da yawa zai iya yin illa ga masu cutar ulsa. Masana kuma sun karyata ikirarin da wasu ke yi musamman a tsakanin Hausawa cewa yawan shan miyar kuka yana toshe basira.
“Kuka sai dai ta kara basira saboda sinadaran da ta ke kunshe da su, kawai camfi ne na Hausawa,” in ji Malama Maijidda.

Daga shafin Aminiya


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN