Kashe ’Yan Arewa a Oyo: Me zai faru da Najeriya ne?


Abubuwa da ke faruwa a jihar Oyo ta Ibadan, abin bakin ciki ne da takiaci wanda babu mai fatan haka ta cigaba da faruwa musamman a karkashin mulkin Muhammadu Buhari, saboda yadda hausawa ko in ce ‘yan arewa suke rasa rayuwarsu da dukiyoyinsu.

Wannan batu abu ne mai dadadan tarihi, ya sha faruwa a lokotun daban-daban can baya, kuma ba a ji dadin faruwarsa ba, sai dai ana ganin kamar an yi wasa da mutunta juna da sauran kabilu ke ayi a wannan yanki.


Sananan abu ne cewa Bayarabe yana da kabilanci, kuma idan ya har ya yi hakuri da wata kabilar da ba tashi ba, to sai idan babu yadda zai yi da hakan sannan zai aimince, amma dai wata rana sai ya tada kayar baya.


Yanzu muna iya kiran yarabawa da masu tada kayar baya, saura kuma wani ya ce mun kira su da ‘yan ta’ada kai tsaye, abin nufi anan shine , wadannan mutanen suna da daurin gindi akan wannan ta’asa da suke yi wa arewa da ‘yan arewa.


Idan ba haka ba, da yanzu mun ga masu fushi da fushin wasu sun dauki mataki, amma yaushe ne Najeriya da shugabaninta suka yi lalacewar da Yarabawa suka fi karfinsu ko kuma suka koma ‘yan lele a wannan gwamnatin da suke kokarin kifarwa da suna zanga-zangar End of SARS?


Ta hanyar yin nazari da dogon tunani kaiwa za a iya gane cewa wane irin mataki ne Yarabawa suka taka a wannan gwamnatin ba su suka kawo ta ba kamar yadda ‘yan arewa ke ikirari ko kuwa sun tsinci dame a kala ne suke shanya yadda suka ga dama?


Dole a yi nazarin irin wadannan matsaloli domin dai koma me zai faru ta tabbata cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya yin komi ba game da wannan kabila da ta samu wuri tana cin kashi ga arewa da kuma ‘yan arewa ana ji kuma ana gani amma an shiru.


Wannan rikici ko harin fin karfi da kabilar Yarabawa ke kaiwa ‘yan arewa abu ne da zamu ce shiryayye, domin kuwa tun kafin a fara kai masu wannan harin wuce gona da iri wasu abubuwa suka rika biyo bayan, sai dai ba a farga da cewa baban al’amarin na nan tafe ba sai da mai kasancewar ta kasance.


Batun gawurtaccen mai tada kayar bayan nan wato Sunday Igboho wanda ya addaibin wannan yanki kuma ga alama yana da daurin gindi wato dai an bashi lasisi ya yi abinda yake so, harma idan yana bukata ya ba fulani makiyaya da ke zaune a wannan shiryya umarnin su bar wannan yanki.


Kai kaji tsabagen rashin ta ido, mutun shi ba hukuma ba, ba sarki ba, ba kowa ba amma yana gargadi ga wata kabila mai matukar mahimmacin a Najeriya baki daya, sannan wanda take taimakawa kabilarsa wajan samar da abubwuan more rayuwa kuma wai ba abinda aka yi masa.


Shi yasa ake tambayar wai wace irin kasa ce muke haka, wadannen irin shugawabannin ne ke jagorantar wannan kasar, shin wai me ke shirin faruwa da wannan kasa ta Najeriya ne?
Dole kuwa ya yi wa kansa wannan tambayar domin idan har mutun bai samu amsa da wuri ba, to ya kuka da kansa ya kuma nemi mafita tun kafin mulki ya kara subulewa ‘yan arewa.
Wannan wulakanci da cin zarafi da ake yi wa kabilar hausawa da ‘yan arewa a yankin Yarabawa fa saboda suna da shugaban kasa ne, idan aka kai lokacin da babu shi, me ake tunanin zai faru ne, kowa ya ga yadda ake yi wa hausawa kisan kare dangi babu tausayi balanta imani.


Shi fada ko rikici yana da bakin tarihi cewa duk lokacin da aka yi shi sai an dauki dogon lokacin kafin kabila ko al’ummar da wannan bala’I ya shafa ta dawo cikin hankalinta har abubuwa su dawo, su cigaba da tafiya kamar yadda suke ada, shi yas aake kaucewa faruwar hakan.
To sai dai, kamar a bangaran gwamnatin wanda take da ruwa da tsaki wajan ganin an zauna lafiya, kai hakkinta ne ma ta samar da tsaro tare da hukunta duk wanda ya nemi tada hankali, amma da yake muna cikin hali ne da ba a san wanda ke mulkin kasar ba ga abinda ke faruwa muna gani.


Kuma gaskiyar magana shi ne, wasu daga cikin ‘yan arewa suna jin dadin abinda ake yi wa hausawa mazauna jihar Oyo Ibadan, kai ka ce dama aka ba su domin rage yawan kabilar hausawa ‘yan arewa.


Kafin in fara bayanin irin bainar da ta bayyana an tafka daga rasa rayuka zuwa dukiyoyi na mutanen arewa a yankin yarabawa da kuma wadanda suka jikkata a sanadiyar wannan cin zalin da yarabawa ke yi wa mutanen arewa a jihar Oyo kuma bisa kulawar shugaba Muhammadu Buhari, zan kawo ba a sin wasu mutanen arewa da suka damu da abinda ya shafi ‘yan arewa.


Mutane irin da Nastura Ashir Sharif sun kware wajan bin diiddigin abu sannan su maganta da zaran abu ya shafi mutanen arewa, saboda haka dole ake jinjina masu game da wannan namijin kokarin da suke yi.


Ina ma ace, irin su ne, za su samu dama da ikon shugabantar al’umma da mutenen arewa ba su kasance marayu ba a lokacin da dan cikin su yake mulki a wannan kasa, kuma lokacin suke yabawa aya zakinta.


Babu shakka Nastura ya yi abinda ya kamata a lokacin da yakamata, domin har gani na yi wasu ‘yan arewa na jiran abinda shugaba Buhari ya saba yi na yin Allah wadai da zaran an zalunci ‘yan arewa, kwatsam sai ga sanarwa cewa gwamnatin Najerirya ta yin Allah wadai da wannan rikici.


Amma fa gaskiyar magana wannan ba rikici bane domin cin zalin da kuma nuna fin karfi, saboda duk wanda ya yi bitar yadda wannan al’amari ya faru zai gane cewa wancan bukatar ta a tashi fulani makiyaya daga wannan yanki ta juya zuwa ga huasawa ‘yan arewa mazauna wannan yanki.


Idan akwai butakar yin dalla-dalla akan wannan bakin al’amari insha’Allahu za ayi domin kara fito da boyayyar manufar da shugabannin arewa suke da ita wajan kitsa wannan fitina.


Idan jama’a za su iya tunawa wannan yanki na yarabawa sun kirkiri wata hukumar tsaro mai suna ‘Amoteken’ wanda ta sha soka daga wasu ‘yan arewa suka hasaso irin wannan fin karfi da aka yi wa ‘yan arewa mazauna yankin Yarabawa da cewa su ma arewa ya kamata su yi wani shigen wannan.


Amma da yake Bahaushe shima yana da na shi hali, sai aka sanya munafurci da gudun wai kadda a batawa shugaban kasa rai, sai kuma yanzu abinda ake gani, yana batawa kowa rai in banda shugaban kasa, abin nufi anan shine idan da wannan abin ya shafi Buhari ya kuma bata masa rai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba.


Idan Allah Ya kai mu sati mai zuwa zan cigaba, kuma zan kawo batutuwa da wasu ‘yan arewa suka yi game da wannan hali ake ciki, sannan idan dama ta bada zan kawo halin da ‘yan arewa da aka rutsa da su a wannan harin fin karfi suke ciki. Allah Ya kawo mana zaman lafiya. Amin summa amin.

Rahotun Jaridar Leadership


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN