1. A yayin da kuka shigo gida, ku gaishe da su ko ma ku rungume su. Hakan zai gina soyayya da darajawa a zukatansu.
2. Ku yi kyakkywar mu'amala da maƙwabtanku kuma kada ku yi munafunci. Kada ku dinga faɗan aibun wasu mutane da kuka haɗu da su kamar direbobi da ma'aikatan kan hanya a gaban su. Saboda yaran nan suna saurare, za su ɗauka kuma za su kwaikwaya.
3. A duk lokacin da kuka kira mahaifanku, ku ƙarfafawa yaranku gwiwa su ma su yi magana da su. A duk lokacin da za ku kai ziyara gare su, ku tabbata kun je da yaran kuma ku mutunta su a gaban yaran. Saboda irin yadda suka ga kuna girmama iyayenku su ma haka za su girmama ku ko su kula da ku.
4. Idan za ku kai su makaranta, kada ku kunna musu waƙoƙi ko kaɗe-kaɗe, a madadin hakan, ku basu gajerun labarai masu ƙarfafa gwiwa hakan yana da matuƙar muhimmanci a gare su- Ku yarda da ni!
5. Ku dinga yi musu tatsuniyoyi, ƙissoshi da tarihin magabata ko kuma karanta musu ko da hadisi guda ɗaya ne a kowace rana. Ba wani lokaci mai tsawo hakan zai ɗauka ba, amma yana da muhimmanci wajen ƙara kusanci da kuma ƙirƙiran tarihin da za a dinga tunawa a tsakanin juna.
6. Ku gyara gashi, ku wanke haƙora kuma ku sa kaya masu kyau ko da kuwa za ku zauna a gida ne. Saboda yara suna buƙatar su fahimci cewa yin tsafta da shiga ta kamala ba wai kawai sai za a je unguwa ake yi ba.
7. Kada ku zama masu zagi ko duka ko kuma ƙorafi akan duk wani laifi da yaranku suka yi. Ku zamo masu haƙuri da kauda kai a wasu abubuwan. Yin hakan zai taimaka sosai wajen gina musu ƙarfin gwiwa da kuma sanin ya kamata.
8. Ku nemi izini kafin ku shiga ɗakinsu. Ba wai kawai ƙwanƙwasawa za ku yi ba, a'a ku nemi izini baki da baki su baku izinin shiga. Suma za su koyi yin hakan yayin shiga ɗakinku ko na wasu.
9. Ku nemi gafara idan ku ka yi wa yaranku laifi, ba su haƙuri da neman gafararsu hanya ce mafi sauƙi ta koya musu bada haƙuri da neman yafiya idan suka yi wa wani ba daidai ba. Sannan hakan zai dasa musu nagarta a zukatansu.
10. Kada ku zamo masu yawan zolaya ko ci wa yaranku fuska ko da da wasa ne akan wasu zantuka ko ɗabi'u ko mu'amala. Hakan na da ƙona rai, in kuna yi musu hakan, to za su taso da tsana da kuma jin haushinku.
11. Lallai ne iyaye su zama masu ba wa sirrin 'ya'yansu muhimmanci sosai.
12. Kada ku yi tunanin za su fahimci ko kuma su ɗauki duk abin da kuka faɗa musu nan take, ku zamo masu haƙuri da naci akan abin da kuke koya musu.
13. Ku dinga yin sallah da addu'o'i tare, ku koya musu yadda ake yi da kanku.
14. Bayan sallar Asubahi, ku zauna da su ku tambaye su irin abubuwan da suke sa ran yi a wannan yinin. Yaran da ba su da jadawalin abubuwan da za su aikata a kowane yini tabbas za su je su taimaka wa wasu wajen gudanar da nasu aikin ko ba mai kyau bane. Sannan hakan zai taimaka wajen koya musu tsara hanyar gudanar da rayuwarsu.
15. Ku yawaita rungumar 'ya'yanku, ku yawaita yi musu addu'a da sa musu albarka a kowace safiya. Hakan na gadar da so da ƙauna tare da gadar da albarka a cikin wannan ahalin.
Ku tuna, wasu iyayen na buƙatar jin irin waɗannan shawarwari, don haka babu laifi don kun tura musu.
Mu so junanmu, domin junanmu.
Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa.
https://www.facebook.com/1047385168698213/posts/3082072048562838/?sfnsn=scwspmo
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari