Duba sunayen sojin saman Najeriya da suka mutu bayan jirginsu ya rikito kasa


A kalla dakarun sojin saman Najeriya 7 ne suka rasa rayukansu bayan rikitowar jirgin sama da suka hau wanda ya tunkari garin Minna da ke jihar Neja.Jaridar legit ta ruwaito.

An gano cewa an sanar da matsala a injin din jirgin wurin 

10:39 na safe amma sai ya tarwatse a yayin da yake sauka a Abuja wurin karfe 10:48 na safe.

Jirgin saman ya tarwatse ne bayan da ya doke wata itaciyar mangwaro, ganau ba jiyau ba suka tabbatar da hakan.

Jaridar Daily Trust ta samu jerin sunayen sojojin da suka rasa rayukansau sakamakon faduwar jirgin saman.

Ga sunayen kamar haka:

1. Flt. Lt. Gazama

2. Flt. Lt. Piyo

3. Flg. Offr. Okpara

4. FS Olawumi

5. ACM Johnson

6. Sgt Oloka

Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Aire Vice Marshal Oladayo Amao ya bada umarnin binciken musabbabin wannan mummunan hatsarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN