Babbar Kotun Tarayya a Najeriya da ke zamanta a Kano ta kori ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar gabanta yana neman ta umarci gwamantin Kano ta cire ɗurin talalar da take yi masa.
Mai Shari'a Lewis Alagoa ya kori ƙarar ce bayan lauyan Abduljabbar, Rabi'u Shu'aibu Abdullahi, ya gabatar da buƙatar mai ƙarar ta janye ƙorafin nasu daga gaban kotun.
Lauyoyin da ke kare gwamnati ba su yi wata-wata ba suka amince da buƙatar kuma nan take mai shari'a ya kore ta.
A ranar Alhamis da ta gabata ne shehin malamin ya shigar da ƙarar da zummar neman kotu ta tilasta wa gwamnati da kwamishinan 'yan sanda da shugaban tsaro na hukumar DSS a Kano da su janye jami'an su da suka girke a kofar makarantarsa da gidansa a unguwar Filin Mushe.
Gwamnatin Kano na tsare da malamin ne a gidansa biyo bayan zarginsa da "kalaman tayar da fitina" game da lamuran Musulunci a farkon watan Fabarairu.
Malamin ya musanta zargin sannan ya buƙaci a haɗa muƙabala tsakaninsa da sauran malamai a jihar, buƙatar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince kuma ya ce gwamnati za ta saka rana da wurin da za a gudanar da ita.
Rahotun BBCHausa
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari