Kebbi: Gobara ta kone gidaje da shago a karamar hukumar Dandi


Gobara ta yi sanadin konesar akalla gidaje 12 da shago 1 a kauyen Tungar Bizo da ke garin Shinko a Kamba da ke karamar hukumar Dandi a jihar Kebbi ranar Laraba 17 ga watan Fabrairu da misalin karfe 5 na yamma kamar yadda wani rahotu ya yi zargi.

Shafin ISYAKU.COM ya samo cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wasa da wuta da yara suke yi, daga bisani sai wuta ta kama wani gida da ke kusa, lamari da ya fadada har ya kama wasu gidaje 11 da shago daya.

Hakazalika, rahotanni sun ce ba a rasa rai a wannan gobara ba, sai dai an rasa dimbin dukiya da ba a kammala kiyastawa ba kafin lokacin rubuta wannan rahotu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN