Kebbi: An kashe mutane 4 da ake zargin masu sace mutane ne a yankin Kende


Rahotanni daga karamar hukumar Bagudo a jihar Kebbi sun ce an kashe wasu mutane guda hudu a yankin garin Kende, wanda ake zargin cewa masu sace mutane ne domin yin garkuwa da su.

Rahotanni sun ce an kama mutanen dauke da bindiga kirar AK47 guda daya da wasu harsasai da ba a fadi yawansu ba.


Hakazalika rahotun ya yi zargin cewa yan Banga ne suka kama mutanen, sai dai mun samo cewa yan Bangan sun nemi agaji daga wasu da ake zargin Yan sa Kai ne daga yankin Mahuta da ke makwabtaka da yankin Bagudo.

An zartar da kisan mutanen guda hudu nan take, kamar yadda rahotanni suka nuna, a yanayi da fusatattun matasa suka kewaye wajen da lamarin ya faru.


Kawo lokacin rubuta wannan rahotu, hukumar yansandan jihar Kebbi bata fitar da rahotu kan lamarin ba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN