Wani dattijo mai suna Hassan Bahago ya rasu sakamakon bugun zuciya bayan yan bindiga sun shiga gidansa suka sace yayansa mata guda biyu a rukunin gidaje na Shagari quarters a garin Funtua, da ke karamar hukumar Funtua a jihar Katsina.
Wannan mumunan lamari ya faru ne ranar Alhamis da dare.
Rahotanni sun ce dattijon, wanda daya ne daga cikin dattijan Mujami'ar ECWA ta Funtua, ya kamu da ciwon zuciya lokacin da Yan bindigan suke janye da shi tare da yayansa mata guda biyu, Saratu da Jennifer, sai ya yanke jiki ya fadi ya mutu nan take.
Yan bindigan sun sace wani ma'aikacin Bankin First Bank mai suna Mr Alex, kuma suka kashe shugaban yan Banga na garin Alhaji Ali Bahago lokacin da ya fito domin ya taimaka wajen dakile harin yan bindigan, amma ya rasa ransa sakamakon harbe harben bindiga tsakaninsa da yan bindigan.
Wani mazauni Shagari quarters mai suna Sagir Muhammed, ya shaida wa Jaridar Thisday cewa yan bindigan sun kai hari a rukunin gidajen da misalin karfe 11:15 na dare, suka tafka ta'asa, suka raunata mutane da dama, kuma sun dauki fiye da minti 30 suna
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari