Jagoran Fulani, Saleh Bayari, ya rasu


Allah ya yiwa wani shahrarren jagorancin Fulani makiyaya kuma dan jarida, Sale Bayari, rasuwa, Jaridar legit ta ruwaito.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Bayari ya mutu ne da daren Alhamis a asibitin koyarwan jami'ar Jos, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Gabanin mutuwarsa, ya kasance shugaban uwar kungiyar Gan Allah Fulani na Najeriya GAFDAN, kuma tsohon Sakataren uwar kungiyar makiyayan Miyetti Allah (MACBAN),

Shugaban GAFDAN na jihar Plateau, Garba Abdullahi Muhammad, ya tabbatar da mutuwar Bayari.

An yi jana'izarsa da safiyar Juma'a bisa koyarwan addinin Musulunci.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN