Da duminsa: Safeton yansanda ya kashe kanshi da bindigarshi


Wani safeton yansanda mai suna inspector Umoh ya kashe kansa ranar Laraba.

Sahara reporters ta ruwaito cewa marigayi Umoh wanda dansandan kwantar da tarzoma ne, ya zo aiki na musamman ne da ake kira special duty a area command na yansanda da ke Birnin Owerri.

Jaridar ta ce Umoh ya koka cewa baya da lafiya. Sai dai babu wanda ya damu. Bayan sun dawo daga aiki ne, sai Unoh ya shiga wani ofis ya rufe kofa, daga bisani sai aka ji karar bindiga.

Jin haka ke da wuya, sai sauran yansanda suka ruga zuwa wannan ofis, amma suka tarar da kofa a rufe daga ciki. Yansandan sun balle kofa, sai dai inspector Umoh ya mutu, Yana kwance a cikin jini bayan ya harbi kanshi a ciki 

Kakakin yansandan jihar Imo Orlando Ikeokwu ya tabbatar ma wakilin Jaridar The Nation da faruwar lamarin. Ya ce kwamishinan yansandan jihar Imo CP Nasiru Muhammed ya bayar da umarnin gudanar da bincike.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN