Ta sa barkono da karfe a al'aurar yar aikin gida har ta mutu, Kotu ta kai uwar yara 4 Kurkuku


Kotun Majistare Mai lamba 8 da ke zamanta a Gyadi Gyadi a Kano, ta tasa keyar wata matar aure mai suna Fatima Hamza kuma mahaifiyar yara hudu zuwa Kurkuku bisa zargin kashe Khadija Rabiu, yarinya mai yi mata aiki a gida da duka, kuma ta sa barkono da wani karfe a alaurarta lamari da ya yi sanadin mutuwarta.

Ana zargin cewa mai yi ma Fatima aiki a gida mai shekara 16 yar asalin jihar Kwara, ta mutu ne sàkamakon duka da Fatima ta yi mata saboda bata yi aikin da ta sa tayi ba kamar yadda ya kamata.


Lauya mai gabatar da Kara na Gwamnatin jihar Kano Barista Asmau Ado,ta gaya wa Kotu cewa an gurfanar da Fatima a gaban Kotun ne bisa zargin kisan Kai, wanda ya saba wa sashe na 224 na dokar Penal code a jihar Kano.

Sai dai Lauya mai kare Fatima Barista Ibrahim Abdullahi Chedi, ya nemi Kotu ta bayar da belin Fatima, ya ce ta yi barin juna biyu da take dauke da shi lokacin da take tsare a hannun yansanda.


Alkalin Kotun Ibrahim Khalil Mahmood, ya ba da umarnin tasa keyar Fatima zuwa Kurkuku, kafin zaman Kotu na gaba ranar 16 ga watan Fabrairu lokacin da Kotu za ta duba takardar neman beli da Lauya mai kareta ya gabatar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN