Wani faifen bidiyo ya nuna yadda jama'a suka kaurace wa shataletalen unguwar Obalande da ke da yawan cinkoson jama'a inda fadan ya barke
Rahotanni sun ce masu fadan suna dauke da makamai da suka hada da bindigogi, adduna, kulake da sauransu. Kazalika akwai zargin cewa an jiyo karar harbe harben bindiga a wajen da aka yi fadan.
Sai dai mun samo cewa soji sun isa wajen da ake fadan kuma sun shawo kan lamarin.
Babu bayanin ko mutum nawa ne suka sami raunuka ko salwantar rayuwa kawo yanzu.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari