Bidiyo: Ku daina kiran yan ta'adda "Criminals" Sheikh Gummi ya gaya wa yan jarida


Sheikh Gummi ya bukaci gidajen jaridu su daina kiran Yan bindiga a matsayin masu aikata laifi ko Kiriminal watau "Criminals". Gummi ya yi wannan tsokaci ne lokacin wata tattaunawa da Yan Jaridar gidan Talabijin na AriseTV ranar Laraba 24 ga watan Fabrairu.

Ya ce idan Yan Jarida suka ci gaba da kiran Yan bindiga a matsayin Kiriminal (criminals) hakan zai iya kara harzuka su kuma su ci gaba da aikata ta'asa. Ya ce, su kansu gidajen Jarida "Criminals" ne saboda kiran Yan ta'adda "Criminals".

Ya ce amfani da zababbun kalamai maau sassauci ga Yan taadda yana da muhimmanci a dai dai wannan lokaci da ake kokarin gano bakin zare wajen ganin an shawo kansu, don su daina aikata barna, su ajiye makamai, kuma su shiga al'umma domin tabbatar da ganin an sami zaman lafiya.

Kalli bayanin Sheikh Gummi a kasa:
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN