An tsinci kwarangwam kai a unguwar Malala a Birnin kebbi jihar Kebbi


An tsinci kwarangwam na kan mutum a unguwar Malala da ke garin Birnin kebbi babban Birnin jihar Kebbi ranar Talata.

Sai dai bayanai daga majiya mai tushe sun ce kwarangwam da aka samu na wata yarinya ce mai suna Wasila diyar Bala Mai tiles wacce ta bace kimanin wata daya da ta gabata a unguwar Malala.


Bayanai sun ce wani yaro mai bola jari ne ya gano wannan kwarangwam wanda aka lullube da gyale aka bizine.

Bayan da labarinya bulla, mahaifin yarinyar ya shaida gyalen diyarsa da ta bace tana sanye da shi.

Tuni dai jami'an tsaro suka fara bincike kan lamarin kamar yadda wata majiya ta shaida mana.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN