Yi wa Lauya duka a Masarautar Zuru ya sa Lauyoyin jihar Kebbi daukan mataki da ya girgiza ma'aikatar shari'a


Shugaban kungiyar Lauyoyi na jihar Kebbi Barista Kabiru Aliyu ya tabbatar da tsunduma da ilahirin Lauyoyi karkashin kungiyar Lauyoyi na jihar Kebbi sun fara kaurace wa Kotuna a fadin jihar daga ranar 3 ga wata Fabrairu har tsawon mako uku.

Barista Kabiru Aliyu ya jaddada haka a wani faifen bidiyo da kungiyar Lauyoyi na jihar Kebbi ta sanar wa gudan Talabijin na kasa watau Nigeria Television Authority NTA ranar Talata a garin Birnin kebbi.

Barista Kabiru ya ce "Abubuwa da dama sun faru a kasar Zuru dangane da tsaro wanda mun yi kira ga Gwamnatin jiha da Masarautar Zuru su dauki maki kan kashe kashe da yan sa kai ke yi


Ya ce "Sun dauki alkawari a fadar Mai Martaba Sarkin Zuru cewa ba za su sake sa hannu a harka da ta shafi shari'a ba. Sai ga shi daya daga cikin manya manyan Lauyoyi wanda muke da, wanda sun yi karatu tare da Chif Justis na Najeriya, sun dauke shi sun bashi kashi a kan wata shari'a da yake tsaya ma wani a Kotu, sun ce idan bai fitar da hannun shi ba a shari'ar za su kashe shi".

Ya kara da cewa "Ganin cewa akwai tsoratarwa da damuwa ga mu masu harkar shari'a bai kamata mu yi kasa a gwuiwa ba saboda kada wani abu a sake faruwa".Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN