An rataye gawar wata matar aure duk da yake ta riga ta mutu, duba dalili


An rataye gawar wata mata bayan ta mutu lokacin da take jiran a kashe ta, ta hanyar rataya a kasar Iran.

Kotu ta sami matar mai suna Zahra Ismaili, da laifin kashe mijinta wanda babban ma'aikaci ne a ma'aikatar leken asiri na kasar Iran.

Sai dai Lauyanta mai suna Omid Moradi, ya yi zargin cewa mijinta yana yawan zagi tare da ci mata mutunci ita da diyarta a ko da yaushe. Sàkamakon haka ta kashe shi ne garin kare kanta.

Duk da haka, Kotu ta yanke wa matar wacce mahaifiyar yara biyu ce hukuncin kisa ta hanyar rataya har ta mutu.

A ranar da za a kashe ta, ta hanyar rataya, an tilasta ta ta kalli yadda aka rataye wasu maza guda 16 har suka mutu a Kurkukun Rajai Shahr da ke kudancin Tehran babban birnin kasar Iran. 

Sakamakon haka zuciyarta ta buga ta fadi ta mutu kafin layi ya kai gareta. Amma duk da haka, jami'an Kurkuku suka aza gawarta a igiya suka rataye ta domin su ba mahaifiyar mijinta damar ture kujera da aka sa a karkashinta domin ta mutu ta hanyar rataya da Kotu ta yi umarni. 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN