An kwantar da jiga-jigan jam’iyyar APC 5 bayan musayar naushi da jefe-jefen kujeru da suka yi

An ba jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar wadanda suka ji munanan raunuka a rikicin da ya barke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar reshen jihar Kwara gado a asibiti Jaridar legit ta ruwaito.

Suna samun kulawar likitoci a wasu asibitoci da ba a bayyana ba a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara, jaridar This Day ta ruwaito.

Daga cikin wadanda aka kwantar sune:

Alhaji Dantala Yaro, ma’ajin jihar

Wahab Adeshina, mamba a kwamitin hukumar jiragen ruwa ta Najeriya (NPA)

MallamLai Karatu, Shugaban matasa

Alhaja Sidi Gidado, mahaifiyar shugabar mata ta jihar

Salihu Elepo, sakataren karamar hukumar Ilorin ta gabas

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a jiharm Hon. Bashir Bolarinwa ya kai wa mutanen ziyarar jaje.

Bolarinwa ya bayyana cewa:

“Ina fari ciki da ganin cewa dukkansu sunyi kwari kuma suna samun dauki.”

A baya mun ji cewa, Bashir Bolarinwa, shugaban riko na jam’iyyar APC a Kwara ya bada labarin yadda aka auka masu da hari a wajen zaman jam’iyya da aka kira a Ilorin.

Bashir Bolarinwa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan an kira su zuwa wajen rajistar da kwamitin Sanata John Danboyi ya ke yi a dakin taro na Banquet Hall.

A cewar Bolarinwa, har zuwa karfe 1:30 na rana, ba a bude wurin da aka ce za ayi taro da karfe 12:00 ba. Wannan ya sa a aikawa Sanata Danboyi sako ta wayar salula.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN