Wakilin VOA Hausa a jihar Adamawa da Taraba ya rasu a hadarin mota


Wani dan jaridar Muryar Amurka (VOA Hausa) dake dauko rahoto daga jihar Adamawa da Taraba, Ibrahim Abdulaziz ya mutu mumunan hadarin motar da ya auku a hanyar Gombe-Alkaleri Jaridar legit ta ruwaito.

Dan jaridar wanda yayi shekara 48 a duniya ya yi aiki da gidajen jaridu da yawa kuma ya yi shirye-shirye a gidajen rediyo irinsu Radio Gotel da FRCN Fombina FM Yola.

Iyalan mamacin sun tabbatar da labarin mutuwarsa, inda suka ce su biyu suka mutu a hadari.

Ya rasu yana da mata uku da yara tara.

Sakataren kungiyar yan jaridan Najeriya, shiyar jihar Adamawa, Fidelis Jocthan; ya yi alhinin rasuwar Ibrahim kuma ya yi addu'an Allah ya jikansa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN