2023: Babu postocin Abubakar Malami don takarar Gwamna a jihar Kebbi - Jibrilu Gwandu


Ministan shari’a Abubakar Malami, ya karyata batun cewa fastocin kanfen dinsa na gwamna sun karade unguwanni a jihar Kebbi, Jaridar legit ta ruwaito.

A cewar jaridar Premium Times, hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Umar Jibrilu-Gwandu a Birnin Kebbi a ranar Juma’a.

Mista Jibrilu-Gwandu na martani ne ga wani rahoton kafofin watsa labarai da ke nuna cewa fastocin kamfen din ministan na 2023 sun karade unguwanni a fadin jihar.

“An janyo hankalinmu zuwa ga wani rahoton karya da ke ikirarin cewa fastocin Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a na neman kujerar gwamna a zaben 2023 sun cika ko ina a jihar.

“Mun karade birnin tare da yan jarida, sun gani da idanunsu cewa babu kamshin gaskiya a rahoton. Bamu ga kowani fosta makamancin haka ba a Birnin Kebbi.

“Don haka, muna so jama’a su yi watsi da wannan labari saboda hasashen mawallafin ne kawai,” in ji shi.

Mista Jibrilu-Gwandu ya bayyana cewa ministan na da magoya baya da dama a jihar da ka iya nuna ra’ayi a kansa, saboda taimakon al’umma da alkhairinsa, inda ya kara da cewa labarin fsatocin kamfen dinsa ba komai bane face kanzon kurege.

“A yanayi da wani zai shirya karairayi da sunan aikin jarida yana bata sunan aikin ne.

“Idan kun tuna, a ranar 16 ga watan Maris, 2020, Malami ya bukaci magoya bayansa da su janye daga batun kamfen din neman takarar gwamnansa na 2023, domin lokaci bai yi ba na kamfen din siyasa kamar yadda yake a dokar zabe na kasa,” in ji shi.

A gefe guda, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bukaci babban jigon jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Tinubu, da ya fuskanci wasu abubuwa masu amfani, inda ya bayyana cewa jam’iyyarsa da shi kansa ba za su ji kamshi shugabanci ba a zaben 2023.

Wike, ya baiwa Tinubu shawarar a ranar Alhamis, a Yola babbar birnin jihar Adamawa yayinda yake rangadi na wani aiki da Gwamna Ahmadu Fintiri ya aiwatar.

Ya ce da wadannan gagarumin kokari da gwamnonin Peoples Democratic Party (PDP) suka yi da kuma gazawar APC karkashin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yan Najeriya ba za su sake kuskuren zabar wata jam’iyya mara alkibla ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN