Matawalle ya haka wa yan bindiga rijiyoyi 138 a jihar Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ce gwamnatinsa ta gina rijiyoyi 138 a sansanonin ’yan bindiga a Jihar da ke fama da matsalar tsaro Jaridar .

Matalle ya bayyana haka ne a yayin da yake jaddada muhimmancin yin sulhu da ’yan binidgar da suka addabi jihar domin a samu zama lafiya.

“Mun san cewa jami’an tsaro ba za su iya dakatar da su ba, mafita ita ce zaunan tattaunawa.“Mun haka rijiyoyi 138 a sansanin ’yan bindiga, kuma ba za mu daina ba har sai mun samar da zaman lafiya,” inji gwamnan, wanda ya cewa wasu na zarginsa da sassauta wa ’yan bindiga.

Ya yi bayanin ne a ganawarsa da malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi wanda ya shiga dazukan Jihar Zamfara domin yi wa ’yan bindiga wa’azi.

Sheik Gumi ya shaida wa gwamnan cewa jagororin ’yan bindiga sun shaida masa cewa zaman lafiya ba zai wanzu ba a Jihar har sai ’Yan Sakai da sojoji sun daina kashe Fulani a Jihar.

“Kwamandojin ’yan bindiga sun shaida min cewa sojoji na kai hare-hare cikin daji kuma hakan ya shafi kowane dangi, kuma a cewarsu dole ne a daina.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN