Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo za su karbi allurar rigakafin. cutar Korona kai tsaye a Talabijin.
Hukumar National Primary Health Care Development Agency, NPHCDA, ta ce za ta samar da ababe da suka wajaba domin ganin hakan ya tabbatar.
Shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shuaibu ne ya sanar da haka lokacin taron manema labarai na hukumar kan cutar Korona ranar Alhamis a Birnin Abuja.
Ya ce yi wa Buhari da Osinbajo allurar rigakafi na Pfizer/BioNTech tamkar fadakarwa ne tare da wayarwa jama'a kai dangane da rigakafin cutar ta Korona a Najeriya.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari