Gwamnatin tarayya ta fadi lokacin da za a gama titin Abuja-Kaduna-Kano


Mista Funso Adebiyi, Shugaban sashin Gini da Gyaran Manyan Tituna, Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje, ya ce za a kammala aikin ginin titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen shekarar 2023.

Adebiyi ne ya bayyana haka lokacin da ya ke duba ci gaban aikin a Kano ranar Juma'a, The Nation ta ruwaito.

Aikin sake fasalin titin Abuja-Kaduna-Kano wanda ake ta samun cigaba za a kammala shi kafin wa'adin wannan gwamnati ya kare.

"Mun gamsu da ingancin aikin kuma muna kokari muga an kara sauri a aikin.

"Kuna iya ganin yadda aiki ke gudana a duka bangarorin titin mai nisan kilo mita 375 daga Abuja-Kaduna-Kano," a cewar sa.

Daraktan ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati a kokarin da ta ke na samar da ingantaccen aiki wanda za a dade ana mora.

Ya kuma roki masu amfani da titi da su ci gaba da hakuri da yanayin titi har zuwa lokacin da za a kammala aikin.

"An samu ci gaba sosai. Saboda an kammala fiye da kilo mita dari duk da ba a jere ba, an kammala bangare na daya zuwa na uku (Abuja - Kano)," a cewar sa.

Ya ce an kammala kilo mita 40 a bangare na biyu (Kaduna-Zaria), da kilo mita 70 karkashin bangare na uku (Zaria-Kano).

"Kuma ana kan kammala bangarori da dama na titin, ana kuma cike guraren da ke da bukatar gyara don saukakawa masu bin titin.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN