Yanzu yanzu: Wani Lauya ya sha duka a hannun wasu mutane a garin Zuru jihar Kebbi, duba dalili


Rahotanni daga garin Zuru a karamar hukumar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi sun yi zargin cewa wani Lauya (Mun sakaya sunansa) ya sha dan banzan duka a hannun wasu mutane ranar Talata 26/1/2021.

Mun samo cewa wasu  mutane ne suka dauke Lauyan suka tafi da shi wani wuri a cikin daji suka yi masa dan Karen duka, lamari da ake zargin cewa yana da nassaba da wata shari'a da aka yi a Kotun Majistare na unguwan Rikoto da ke garin Zuru.

Mun kuma samo cewa wasu Lauyoyi da ke garin Zuru sun ki fitowa aiki da safiyar ranar Laraba 27/1/2021 saboda nuna takaicinsu ga abin da ya faru da abokin aikinsu. Sai dai mun gano cewa lamarin ya lafa bisa wasu dalili na shigowar manya.

Akwai rade radi mai karfi cewa a lokacin rubuta wannan rahotu Lauyan tare da wasu mutane suna tattaunawa kan lamarin. 

Sai dai har lokacin rubuta wannan rahotu, hukumomi a jihar Kebbi basu fitar da jawabi kan lamarin ba kawo yanzu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN