Rundunar sojin Najeriya ta tura soji mata guda 300 domin gudanar da aikin tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna Channels TV ta ruwaito.
Wannan shi ne karo na farko da aka tura soji mata zuwa aikin tsaro a cikin harkokin tsaro na jihar Kaduna.
Gwamna Nasir El-rufai ya yi maraba da wannan tsari. Ya ce yana da yakinin cewa za a yi nassara wajen ganin an kakkabe yan bindiga da miyagu da ke addaban jama'a mazauna wannan yankin da matafiya da ke bi ta hanyar zuwa Abuja.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari