Yanzu yanzu: Ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi sun fara yajin aikin gama gari


Ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin kungiyar kwadago na jihar Kebbi sun fara yajin aiki a fadin jihar.

Wata takarda da kungiyar kwadago na jihar ta fitar ya ce an fara yajin aikin ne da karfe 12 na safiyar ranar Laraba 6 ga watan Janairu 2021.


Takardar ta bukaci Gwamnatin jihar Kebbi ta biya ma'aikatan jihar da tsarin mafi karancin albashi na N30,000 da neman a biya wadanda suka yi ritaya daga aiki tun 2017 hakkokinsu.

Kazalika takardar ta bukaci Gwamnatin jihar Kebbi ta biya kudaden hutu na ma'aikatan jihar da ke matakin albashi na 7 zuwa sama tun 2019 zuwa 2020.


Yunkuri da muka yi na jin ta bakin shugaban kungiyar kwadago na jihar Kebbi da Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi kan làmarin ya ci tura sakamakon wasu dalilai kafin lokacin rubuta wannan rahotu.Hatta Sakatariyar Gwamnatin jihar Kebbi da sauran ma'aikatu an rufe kofar shiga da sarka da kwado, kuma ma'aikatan sun kaurace wa ofisoshinsu. Hatta ma'aikatan shari'a da Kotuna sun kasance a rufe.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN