Shekara 47 da aure, Balaraben Saudi bai taba ganin fuskar Matarsa ba


Zai yi wahala ka yarda cewa an yi shekaru 47 da yin aure, amma mai gida bai taba ganin fuskar matarsa ba, har kuma ta haifa masa ‘ya ‘ya goma.

Hakan ta tabbata, kwanakin baya wani bidiyo na wani mutumi ya bayyana, inda ya shaidawa Duniya cewa bai taba ganin fuskar uwargidarsa ba.

Jaridar Life in Saudi Arabia ta ce wannan Bawan Allah da ya yi aure ya na saurayi shekaru 47 da su ka wuce har ya zama tsoho tukuf a halin yanzu.

Duk tsawon wannan lokaci, wannan mutumi bai taba ganin ya fuskar sahibar ta sa ta ke ba.

Da aka tambayi wannan mutum ko menene dalilinsa na haka, sai ya ke cewa shi mutumin da ne, don haka bai yarda mace ta rika bayyana fuskar ta ba.

Wannan dattijo ya ce uwargidarsa ba ta bayyanawa kowa fuskarta a Duniya, kuma haka suke zaune ko da cewa ba shi ne ya tursasa mata yin hakan ba.

Da ake hira da wannan mutum, ya tabbatar da cewa akwai wasu kabilun Larabawa a bangaren kasar Saudi Arabiya da ba su taba bari a ga fuskarsu.

Sai dai shi kan shi wannan mutum mai ‘ya ‘ya 10 ya shaidawa ‘dan jaridar cewa wannan al’ada ta su, ta sabawa addinin musulunci da ake bi a yankin.

A cewarsa, mutane da dama sun yi fatali da wannan al’ada da ta hana mata fito da fuskokinsu, amma ya ce har gobe akwai wadanda su ka yi riko da ita.

A kasar Hausa kuma, labarin da mu ke samu shi ne wasu samari da ‘yan mata sun huro wuta, suna so a kashe lefe da kayan aure da aka saba yi a yankin.

Yaran zamanin sun bijiro da maganar iyaye su yi fatali da al'adar da aka saba yi wajen aure.

Wadannan matasa masu bibiyar shafin Twitter su na ikirarin cewa wadannan al’adu ba su da wani amfani sai jawo rayuwar karya da kokarin son a burge.

Source: legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN