Yanzu yanzu: Jami'an tsaro a Kebbi sun fara kama masu kashe jama'a da sunan sa kai a Masarautar Zuru


Rahotanni da dumi dumi daga garin Kanya da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a kudancin jihar Kebbi sun tabbatar cewa motoci uku cike da jami'an soji da wasu motoci makare da jami'an yansanda sun dira garin Kanya da yammacin ranar Juma'a 22/1/2021 domin zakulo bata gari da ke kashe kashen jama'a da sunan Sa Kai a kasar Zuru.

Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo cewa jami'an tsaro sun kama wani jigon yan sa Kai a kauyen Dgoga da ke kusa da garin Kanya, daga bisani sun nufi kauyen Gwazawa da ke makwabta da garin Kanya domin gudanar da aikinsu.

Sai dai mun tattaro cewa wasu Yan Sa Kai sun yi gangami dauke da makamai sun datse hanyar Gwazawa, amma daga bisani mun gano cewa sojin sun zarce zuwa garin Wasagu.

Wata babban majiyar tsaro a jihar Kebbi, ta tabbar cewa shugĂ ban Yan sa Kai na kasar Zuru Mr John Mani, ya ce wasu bata gari ne ke gudanar da kashe kashen jama'a komabayan dalilai da ka'idodin aikin sa Kai sakamakon haka ya nisanta Yan sa Kai na ainihi daga wadannan mutane.

Mun samo cewa sakamakon haka ya sa hukumomi suka fara aikin tabbatar da doka da oda a kasar Zuru.

Yayin rubuta wannan rahotu, yanzu haka, mun samo cewa Yan sa Kai goye da junansu a kan babura na ta tururuwa dauke da makamai kamar yadda suka saba, kuma wasu da dama sun nufi garin Wasagu duba da cewa motocin soji sun nufi garin Wasagu

Ana zargin yan sa kai da wuce wuri ta hanyar kashe jama'a marmakin fuskantar yan bindiga da masu sace mutane da shanaye da ke addaban jama'a wanda shi ne dalilin kafa kungiyar sa kai.

Bayan jerin kashe kashe wanda ya hada da kisan da ake zargin sun yi a baya bayannan a garin Ribah da kashe wani gurgu kuma jigo a kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar Kebbi, AlhaJi Mande Kanya, wanda aka yenke shi ta keya har aka gundule kansa bayan an yi zargin cewa wadanda ake zargin ne suka dauke shi daga gidansa a cikin iyalinsa suka je suka kashe shi a daji kusa da kauyen Tungar Wewe Yan makonni da suka gabata.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN