Ƴan bindiga sun sace Mai Unguwa a Katsina, sun raunata ƙaninsa


Yan bindiga, a safiyar ranar Juma'a sun yi awon gaba da Mai Unguwar garin Raddah a karamar hukumar Charanchi na Jihar Katsina, Alhaji Kabir Umar, The Punch ta ruwaito.

Sun kuma raunta ƙaninsa mai suna Aminu a cinyarsa. A halin yanzu yana asibiti a Katsina ana kulawa da shi.

Mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun afka garin misalin ƙarfe 2 na dare suka shafe awanni suna ta'addi.

A halin yanzu mazauna garin ba za su iya tantance adadin abubuwan da ƴan bindigan suka sace ba.

Daya daga cikin mazauna garin da ya nemi a sakayya sunansa ya ce, 'ƴan bindigan sun shigo kauyen misalin ƙarfe 2 na dare suna ta harbe-harbe.

"Sun tafi da Mai Unguwar mu sun kuma raunata ƙaninsa a cinya. Amma ba za mu iya cewa ga adadin abinda suka sace ba domin suna ta harbe-harbe yayin da suke satar da kuma lokacin da za su tafi."

Majiyar ta kara da cewa har zuwa safiyar ranar Juma'a ba san inda mai unguwar ya ke ba.

Kakakin yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai bada cikakken bayani ba.

"Da gaske ne", a cewarsa ta wayar tarho.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN