Yan sa Kai kimanin 500 sun kewaye sansanin soji Sarkin Wasagu ya sa baki


Rahotanni daga garin Wasagu da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a kudancin jihar Kebbi sun nuna cewa Yan sa Kai kimanin 500 sun kewaye sansanin soji da ke Wasagu suna neman soji su saki yan sa Kai da suka kama.

Da yammacin ranar Juma'a 22/1/2021 ne soji cikin motoci guda uku suka kama wani Dan sa Kai a wani kauye kusa da garin Kanya, daga bisani suka zarce zuwa kauyen Gwazawa domin damke wani Dan sa Kai, daga bisani suka zarce zuwa sansaninsu da ke Wasagu.

Rahotanni sun nuna cewa Yan sa Kai sun bukaci soji su saki yan sa Kai da suka kama. Sai dai Sarkin Wasagu ya sa baki kan lamarin Wanda hakan ya sassauta zafi da lamarin ya haifar.

Sai dai kawo lokacin rubuta wannan rahotu, babu wani cikakken bayani kan makomar Yan sa Kai da soji suka kama.

Amma wata jita jita da ke yawatawa sun yi zargin cewa an wuce garin Birnin kebbi da wadanda aka kama. Lamari da babu tabbaci a kansa kawo yanzu.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


2 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. A gaskiya ya kamata idan yan sa kai suka kama wanda ake tuhuma su hannuntashi ga hukuma domin bincike. Allah Ya kawo muna ƙarshen wannan fitina.

    ReplyDelete
  2. Gaskiya ne Sirajo

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN