Rundunar yansandan jihar Ondo ta kama wani dan sanda sabon dauka mai suna David Friday, da wani soja mai suna Innocent Victor bisa zargin aikata fashi da makamai.
Kwamishinan yansandan jihar Ondo. Bolaji Salami ya shaida wa manema labarai haka ranar Alhamis 21 ga watan Janairu.
Ya ce dansandan ya aiki ne a ofishin yansanda na Olofin a karamar hukumar Idanre a jihar Ondo.
Ya ce shi kuwa sojin yana aiki tare da 32 Artillery Brigade, Nigeria Army, Owena Cantonment, Akure.
Ya ce an kama dansandan da sojin ne a mahadar Ojadale a Idanre lokacin da suke yi was jama'a fashi.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari