Yan bindiga sun halaka wani babban hafsan soji a jihar Zamfara


Yan bindiga sun halaka wani babban hafsan soji mai suna Lt. JF London a wani kwanton bauna da suka yi wa soji a garin Janbako da ke karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara ranar Lahadi jaridar Sahara reporters ta ruwaito.

Jaridar ta kara da cewa wasu soji biyu sun sami raunuka a harin.


Rahoton ya ce maharan sun diran wa sojin ne a cikin motocin Hilux da babura yayin da sojin ke kan hanyarsu ta zuwa cikin garin Janbako wajen aikin kwantar da fitina bayan yan bindiga sun farmaki al'umma a garin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN