Tsohon mai shekaru 80 ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matashiya 'yar 33


Wani tsoho dan shekara 80 ya mutu a wani lamari mai rikitarwa a wani masauki da ke Dar es Salaam, Tanzania, bayan ya shafe dare da wata matashiya mai shekara 33.

An tsinci David Mluli matacce a ranar Asabar, 16 ga watan Janairu, a daki mai lamba 22 a Mbezi Garden, inda ya je shakatawa da wata mata mai suna Neema Kibaya (33) wacce tuni aka kama ta kan mutuwarsa.

Kwamandan yan sandan yankin Kinondoni, Ramadhan Kinai ya tabbatar da labarin bakin cikin kamar yadda The Citizen ta ruwaito.

Shugaban yan sandan ya ce:

“Yan sanda sun isa yankin sannan suka tsinci gawar Mista Mluli tare da wata mata wacce ta bayyana kanta a matsayin Neema Kibaya. Kibaya ya fada ma yan sandan batun alaka ta soyayya da ke tsakaninta da marigayin.”

Jami’an sanye da inifam sun dauki gawar mamacin zuwa asibitin Mwananyamala don yin gwaji saboda gano abunda ya haddasa barinsa duniya.

Ba a zargin wani abu

A bisa ga binciken fari, babu wani abu da ake zargi kuma ta iya yiwuwa Mluli ya yi mutuwar Allah ne.

Kingai ya bayyana:

“Babu wani alamu da ke nuna kokwanto kan haka ill an gano gajeren bujensa a jike kafin ya mutu.”

A wani labari na daban, wata hadimar Gwamnan jihar Ebonyi tayi murabus daga gwamnatin.

Hadimar wacce kafin murabus dinta take a matsayin babbar mai bayar da shawara ga gwamnan kan ci gaban kasuwanci ta bayyana dalilinta na ficewa daga gwamnatin.

A wasikar murabus dinta mai kwanan wata Laraba, 30 ga watan Disamba, 2020, wanda Legit.ng ta gano, Deaconness Udeakaji ta bayyana cewa murabus din nata ya zama dole domin tsiratar da aurenta.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN