Wani tsohon Minista dan jihar Kebbi ya rasu


Bala Bawa Ka’oje tsohon Ministan Wasanni, ya mutu yana da shekaru 60.

A cikin wata sanarwa mai taken ‘Tsohon Ministan Wasanni Ka’oje ya mutu yana da shekara 60, aka binne shi a Abuja" a ranar Talata, kakakin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Ademola Olajire, ya ce ’yan uwa a fannin wasanni a kasar sun shiga cikin jimami da mutuwar Ka’oje.

NFF ta samu wakilcin Babban Sakatare, Dokta Mohammed Sanusi da Shugaban Kungiyoyin Membobi, Ali Abubakar Muhammed.

An binne gawarsa a Abuja a ranar Talata da rana.

Sanusi ya bayyana marigayin a matsayin "ma'aikacin gwamnati mai kima da rashin girman kai wanda ya nuna matukar kwazo da sha'awar ci gaba da kuma bunkasa wasannin Najeriya."

Bala Bawa Ka’oje wanda aka haifa a Kebbi a ranar 20 ga Satumba 1960, ya sami digiri na biyu a kan Injiniyan gini daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

A wani labarin daban, Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom, Udo Ekpenyong ya rasu. Ekpenyong ya rasu a ranar Litinin a Uyo kamar yadda wani jami'in gwamnatin jihar Akwa Ibom ya tabbatarwa da Premium Times a ranar Talata da safe.

Jami'in wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce shugaban jam'iyyar PDP din ya rasu ne sakamakon fama da yayi da cutar korona.

Sources: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN