Ta kunduma wa Sarki zagi, duba hukunci da Kotu ta yi mata


Wata kotun kasar Thailand a ranar Talata ta yankewa wata mata 'yar shekara 87, Anchalee Preelert, hukuncin shekaru 43 a gidan yari kan laifin daura hotuna a yanar gizo da ya batawa Sarkin kasar suna.

Amma daga baya kotun ta rage hukunci zuwa rabin abin aka yanke da farko saboda ta amince da aikata laifin, bisa takardun kotu da jaridar dpa ta gani.

Laifin zagin sarki na da daya daga cikin hukunci mafi tsauri a duniya kuma mutum zai iya shekaru 15 a gidan yari idan aka kama shi da laifin.

An kama Anchalee Preelert, da laifuka da dama na zagin sarki da saba dokokin amfani da yanar gizo ta hanyar daura bidiyoyin da ka iya lalata mutuncin gidan sarauta.

Mutan kasar Thailand sun gudanar da zanga-zanga kan hakan inda suke kira ga canza dokokin kasar zuwa na demokradiyya

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN