Gwamnatin Buhari na Shirin shigowa da maganin Korona daga kasar China


Gwamnatin tarayya ta ce ta fara magana da gwamnatin kasar Sin da nufin samun magungunan cutar nan ta COVID-19 ga mutanen Najeriya.

Ministan harkokin kasar wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, ya bayyana wannan a lokacin da ya yi magana da manema labarai jiya a garin Abuja.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta ce Geoffery Onyeama ya zanta da ‘yan jarida ne bayan ya gana da takwaransa na kasar Sin, Wang Yi.

Mista Wang Yi ya kawo ziyarar aiki zuwa Najeriya domin ganin yadda Sin za ta taimakawa kasar.

Ministan harkokin kasar wajen ya bayyana cewa Sin ta taimakawa Najeriya matuka tun da aka fara fama da wannan annoba ta hanyar bada kayan aiki.

Onyeama ya ce a halin yanzu akwai kasashen da su ke kokarin gano maganin cutar, daga ciki har da kasar Sin, kuma Najeriya za ta nemi taimakonta.

“Muna samun gudumuwa sosai daga kasar Sin a bangaren bada kayan aikin likitoci na PPE, sun yi maza sun taimaka mana da kayan.” Inji Onyeama.

Ya ce: “Sin ta na cikin kasashen da ta gano maganin COVID-19, saboda haka muna magana da ita ta taimaka mana da magungunan saboda mutanenmu.”

Daily Trust ta rahoto Ministan yana bayanin niyyar Najeriya na ganin an rika samun jirgin sama wanda zai rika tashi kai tsaye daga Najeriya zuwa Sin.

Shugaban kwamitin PTF, Boss Mustapha ya bayyana cewa an yi wa masu NYSC fiye da 35, 000 gwajin COVID-19, kuma an gano 731 sun kamu da cuta.

PTF ta ce an samu masu hidimar kasa daga duka Jihohi 36 da ke dauke da COVID-19

Da yake jawabi a ranar Talata, Mista Boss Mustapha ya ce kwamitin PTF ya yi amfani da gwajin gaggawa na RDT a kan wadanda NYSC ta ke yi wa horo.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN