Kebbi: Yan bindiga sun kashe mutune 26, soji 2,sun kone gidaje a Masarautar Zuru


Rahotanni daga Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi sun tabbatar cewa yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Munhaye da ke karkashin garin Bena a karamar hukumar Danko-Wasagu suka kashe mutum 26. Kazalika sun kashe soji biyu suka raunata soji uku, kuma suka dauke bindigar da aka girka a kan motar soji daga bisani suka banka wa motar sojin wuta kuma suka kone gidaje.a kauyen da yammacin ranar Asabar 23 ga watan Janairu.

Bayanai sun ce uku daga cikin sojin da aka raunata suna jinya a wani Asibiti a garin Birnin kebbi

Rahotanni sun ce maharan wanda ake zargin sun fito ne daga jihar Zamfara su kimanin 500 a kan babura dauke da bindigogi sun kai hari a kauyen Munhaye ne da misalin karfe 4 na yamma, kuma suka tafka mumunan ta'asa.

Wasu gawaki da aka samu suna da raunukan harbin bindiga wasu kuwa an sassare su ne da adduna.

Sai dai mun samo cewa 17 daga cikin gawakin yan garin Dabai ne Manoma da suke zaune a garin Munhaye domin dalilin yin noma kafin su gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga.

Wata majiya ta shaida mana cewa Yan sai Kai sun kai wa soji dauki kuma suka fuskanci yan bindiga, lamari da ya haifar da bata kashi tsakanin bangarorin guda biyu.

Sai dai majiyar ta ce yan bindiga sun riga sun tafka ta'asa mai yawa bayan kone gidaje da dukiya, sun kone motar soji, suka dauke bindigar da aka girka a motar soji, suka kone wasu motocin bayin Allah kuma suka kawo gawakin suka jera a kan hanya.

Kazalika mun samo cewa Yan sa Kai sun kwashe gawakin manoman yan garin Dabai da Yan bindiga suka kashe suka loda su a motar Kanta, kuma aka tafi da su garin Dabai. Lamari da ya sa hankulla suka tashi kuma aka yi kisan ramuwar gayya kan wasu mutane biyu. Mun samo cewa, ana zargin an sake kashe wani mutum da daren Lahadi bayan ya je daukan hotuna.

Mun samo cewa yanzu haka Yan sa Kai sun bazama cikin daji domin bincike da sintiri.

Masarautar Zuru ta fada cakwakiyar matsalar rashin tsaro gadan gadan, irinsa na farko a tarihi, kuma babban kalubalen tsaro ga Gwamnatin jihar Kebbi.




Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN