Gobara ta tashi a makarantar horar da kuratan soji na Depot da ke Zaria a jihar Kaduna da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar.
Gobarar ta kama gini na 15, amma an shawo kan gobarar a cewar mataimakin daraktan kula da harkar labarai na makarantar Captain Audu Arigu.
Arigu ya gaya wa TVC News cewa an sami nassarar shawo kan gobarar ne sakamakon daukin gaggawa na hadin gwiwa tsakanin sashen kashe gobara na makarantar da na sashen kashe gobara na jihar Kaduna. Ya ce ba a rasa rai ba lokacin gobarar.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari